Limamin Masallacin Ka’abah Sheikh Adil Alkalbany Ya Koma Yin Fim – Labarai.com.ng
Limamin Makkah Sheikh Adil Alkalbany Ya Koma Yin Fim.
Tsohon Limamin masallacin Ka’abah Sheikh Adil Alkalbany ya bayyana a cikin wani guntun bidiyo tare da wasu “Yan fim inda sukayi Wani Shirin fim mai salon talla.
Sheikh Alkalbany tuni ya bayyana aniyarsa ta shiga masana’antar Hollywood inda yake cewa ya dace da yin sana’ar fim bayan wasu sunce bai dace da yin sana’ar ba har ya bayyana a wani gajeran faifan bidiyo.
Haka zalika,ko a kwanakin baya anan gida Najeriya akwai mawakin da bayyana cewa sana’ar yin fim da wake yafi fadakarwa sama da yin wa’azi.
Wata kila shima Malamin abunda yayi amfani dashi kenan.
Haka dai ko a kwanakin baya an gano malamin a gurin buga karta yana aikata wasan.
A da’awar Malamin yace “Dole ne adding musulunci ya canza salo domin sauya hanyoyin dakile tsattsauran ra’ayin da yake saka mutane su shiga harkar Ta’addanci”.
Mene ra’ayin ku akan Malamin?