Kasuwanci

Kwamfanin Coca-Cola ya maka Kwamfanin Pop-Cola a kotu bisa zargin kwaikwayon fasaha ta fannin suna, tambari da tsarin tallace-tallace.

Kwamfanin Coca-Cola ya maka takwaransa na Pop-Cola babbar Kotun Jihar Kano sakamakon kwaikwayo ta fannin zanen tambari da tallace-tallace.

Kamar yadda kuka sani, Kwanfanin na Pop-Cola dai an ƙaddamar da shi ne a watan Yulin wannan shekarar tare da wasu fitattun mutane ciki harda Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Kano Focus ta wallafa yadda Kwamfanin na Coca-Cola yake zargin Kwamfanin Mamuda Beverages wanda aka fi sani da Pop-Cola ta fannin ƙirƙirar zanen tambari da yayi kamanceceniya da nasu.

A cewar Coca-Cola, sune na farko a Nigeria da suka fara ƙirƙirar suna da tambarin Kwamfaninsu na musamman wanda duk sauran reshensu a ƙasashen Duniya ma a haka aka fi saninsu.

Bayan fara gudanar da zaman kotun, a ƙarshe Mai shari’ah, Muhammad Nasir-Yunusa ya dage ƙarar zuwa 11 ga watan Disamba domin cigaba da jin hujjoji daga ɓangarorin biyu.

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!