Labaran Duniya

Kungiyar Taliban Sun Haramta Jin Waka Da Ragewa Mata Hanya A Mota Dole Saida Muharraman Su – Labarai.com.ng

 Ƴan Taliban a Afganistan sun hana rage wa mata hanya zuwa wani wuri mai nisa face suna tare da wani ɗan uwansu namiji.


Ma’aikatar inganta dabi’u da kare hakkin bil’adama ta Taliban ta ce idan ma za a rage wa matan hanya to ya kasance waɗanda ke sanye da niƙabi ne, kuma suka suturta jikinsu baki ɗaya.

Masu fafutuka sun ce Taliban ba ta fayyace ita a wurinta me take nufi da hijabi ba, tunda dama galibin matan Afganistan suna sanya hijabi.

Har ila yau Taliban ɗin ta bukaci mutane su kauce wa jin kida a motocinsu yayin da suke tafiya.

Wannan sabon umarni ya zo ne makonni bayan da ƙungiyar ta buƙaci gidajen talabijin da su daina nuna sabulu da wasan kwaikwayo da ke dauke da ’yan fim mata.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!