Siyasa

Kungiyar ƴan Arewa mazauna yankin Inyamurai sunyi kira a goyawa ɗan ƙabilar Igbo baya ya zama Shugaban ƙasa a 2023.ɓ

Ƙungiyar dattawan Arewa mazauna yankin Inyamurai (Igbo) sun nuna goyon bayansu akan a baiwa ɗan ƙabilar Igbo dama ya zama Shugaban Nigeria a zaɓe mai zuwa, 2023.

Mista Umaru, ɗaya daga cikin wakilan wannan ƙungiya ya bayyana cewa “abune mai matuƙar mahimmanci a baiwa ɗan ƙabilar IGBO dama ya zama Shugaban ƙasa a karo na gaba.

A cewarsa, ƙungiyar tasu ba domin muradin siyasa aka kafata ba, kuma ta ƙunshi ƴan Arewa ne kaɗai mazauna yankunan na Inyamurai؛

Yankin Arewa da Kudu maso kudancin Nigeria duk sun Shugabanci ƙasar nan. Don haka wannan loƙacine da ya kamata mu baiwa ɗan ƙabilar IGBO dama, Inji Umaru.

Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta wallafa” Malam Umaru yayi ƙira na musamman ga ɗaukacin mutanen Arewa akan su marawa ƴan ƙabilar Igbo baya domin a samu shugaban ƙasa daga yankin, saboda acewarsa suma ƴan Nigeria ne masu cikakken iko.

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!