Ku gaggauta janye tallafin man-fetur zuwa nan da wata shida. ~Bankin Duniya ya gargaɗi Nigeria
Babban Bankin Duniya ya gargaɗi Nigeria cewa ta gaggauta cire tallafin man-fetur nan da wata shida masu zuwa.
Ya kuma shawarci cewa kafin cirewar a tabbata an samar da shiri na musamman da zai taimaka wajen haɓɓaka darajar farashin na man-fetur a Nigeria.
A cewar binciken da Bankin Duniya ya gudanar, cikin kaso 40% na talakawan Nigeria, kaso 3% kawai suke amfana da tallafin na man-fetur da ake fitarwa.
Bankin na Duniya da Kungiyar tattara kuɗaɗe ta Duniya (IMF) sune manya-manyan ƙungiyoyin da suka shawarci Nigeria cikin watan Nuwamba akan su cire tallafin man-fetur.
A ƙiyasti, Nigeria ta kashe aƙalla dalar Amerika $2.1 dai-daida naira biliyan 864 cikin wata tara game da tallafin man-fetur.
A gefe guda kuma, Ministar kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa wato Zainab Ahmed, ta bayyana cewa ko a cikin kasafin kuɗin shekara mai zuwa 2022 babu kuɗirin tallafin man-fetur kuma wannan yana cikin shirye shiryen janye tallafin؛