Uncategorized

Kotu ta ƙi bayar da belin ɗan jarumi Shah Rukh Khan

 Kotu ta ƙi bayar da belin ɗan fitaccen jarumin nan na fina-finan Indiya na Bollywood Shah Rukh Khan, kwana 18 kenan bayan kama shi kan zargin da ake mishi na mu’amala da miyagun ƙwayoyi a wajen wata liyafa da aka gudanar.

An ɗauki Aryan Khan mai shekara 23 a cikin wani babban jirgin ruwa da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Goa daga birnin Mumbai ranar 2 ga watan Oktoba,sannan

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na kasar India din  ta tuhume shi a ƙarƙashin dokokin “mallaka da amfani da kuma sayar da miyagun ƙwayoyin” na kasar.

Ya yi watsi da dukkan zarge-zargen da ake yi masa tun a ranar farko.

Lauyansa Satish Manshinde ya sha nanata wa kotun cewa ba a samu komai a tare da ɗan jarumin ba, “kuma babu wata shaida da ke nuna cewa ya sha wata muguwar ƙwaya.”

Haka dai;

Amma wata kotu a Mumbai a yau Laraba ta yi watsi da batun ba shi beli a karo na biyu. Ta fara watsi da batun ba da belin nasa ne ranar 8 ga watan Oktoba.

Sannan kotun ta ƙi bayar da belin wasu sauran mutum biyu da su ma ake tuhumarsu.

Ana sa ran lauyoyin Aryan Khan za su ɗaukaka ƙarar matakin a babbar kotun Mumbai.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!