Labarai/Addini

Ko a jiya sai daya gabatar da karatu duk da bashi da lafiya (Abubakar Giru Argungu)

MAZAN JADDADA SUNNAH AN KWANTA DAMA 😭😭

Sheikh Abubakar Giru Argungu

Jiya Talata war haka ajalin jinya bata kama Malam Abubakar Giro Argungu ba, domin ya gudanar da karatu bayan sallar magrib zuwa isha

 

Bayan gama karatu yana komawa gida jinyar ajali ta riskeshi, ya koma ga Mahaliccin mu awa daya da suka wuce da nake wannan rubutu

 

Malam Abubakar Giro Argugun Malamina ne kuma tamkar Uba a gareni, Ya na Kaunata Saboda Allah, yana yawan kirana mu tattauna akan matsala na tsaro

 

Na fara magana da Malam lokacin da masu garkuwa da mutane suka kama Alaramma Sheikh Ahmad Ibrahim Suleman Kano, na bawa Malam shawarwari ta fuskar tsaro akan yadda Malamai zasu kare kansu tunda Gwamnatin Demokaradiyya ba zata iya basu kariya na tsaro ba

 

Wannan mutuwa na Malam ta girgizani matukar girgizawa, duniyar Musulunci ba zata manta da Malam ba, haka tarihin gwagwarmayar kungiyarmu na Izala ba zai cika ba sai an saka sunan Malam Abubakar Giro Argungu

 

Malamai sukace idan Allah Ya na so ya dauke albarkan ilmi a cikin mutane sai ya dauke Malamai, hakika Allah Ya dauke mana ilmin da ba zamu iya maye gurbinsa ba

 

Malam Abubakar Giro Argungu ya ga jiya ya ga yau, ya kare rayuwarsa yana mai hidima wa addinin Allah, muna kyautata masa zato ya dace da kyakkyawan karshe Insha Allah

 

Yaa Allah Ka jikan Malam

Yaa Allah Ka kula da iyalan Malam

Yaa Allah Ka saka masa da Aljannah Madaukakiya 😭😭😭

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!