Al'ajabi

Kiyi Hakuri Shaidan Ne Ya Ribace Ni, Magidanci A Jihar Kano Ya Bawa Matarshi Hakuri, Bayan Ya Dirkawa ‘Yar Kanin Shi Cikin Shege

 

Majiyarmu ta samu wani labari daga shafin Facebook mai suna Daily news hausa sun ruwaito cewa wani magidanci cikin shege wanda abun baiyi dadi ba ga yadda takasance.

“Wani magidanci dake zaune a karamar hukuman Dala dake jahar Kano, ya dirkawa wata marainiya wacce take ‘ya a gurinshi ciki, wacce yarinyar tana da kimanin shekara 15 a duniya, inda ya ribaceta da lemun kwalba.

An ruwaito cewa kafun ya bata lemun sai da ya kwaya aciki sannan ya bata nan take ta kama bacci shi kuwa ya afka mata.
Bayan sati Biyu da faruwan lamarin matar sa wacce take rike da yarinyar, ta fara ganin wasu alamu a tattare da yarinyar, inda ta garzaya asibiti da yarinyar don yi mata gwaji, anan ne aka tabbatar mata da ‘yarta tana da juna biyu inda suka takura yarinyar ta fada, sai ta amsa da cewa Baba ne.

Magidancin ya shaidawa matar tashi cewa tayi hakuri lallai shedan ne ya ribance shi kuma hakan ba za ta sake aukuwa ba.
Daga Muhammad Inuwa Zaria”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!