Labaran Duniya
Trending

Karshen Duniya: Yadda wani yaro ya cirewa Abokin sa ido domin hada Layar bata a Kano

Wani matashi ya cirewa wani yaro ɗan shekaru 12 Ido don a haɗa masa layar ɓata.

 

A yau ne kakakin yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cafke wani Matashi mai suna Musa Hassan mai shekaru 17 da zargin cirewa wani yaro ido a Unguwar ɗan tsinke dake ƙaramar hukumar tarauni dake Kano.

Wanda ake zargin ya shaidawa yan sanda cewa ya naimi abokinsa ne daya kai shi gurin da za’a haɗa masa layar ɓata, shi kuma abokin nasa sai ya kaishi wajan wata kakarsa mai shekaru 100 (a yadda ta faɗa) domin tayi masa wannan aikin.

 

Wanda ake zargin ya shaifa mana cewa matar ce ta umarce shi da ya kawo mata idon mutum domin haɗa wannan layar, shi yasa shi kuma yaje ya samu wani almajiri ya kaishi wani guri inda yayi amfani da wuƙa ya kwakwale masa idon sa na dama. bayan ya kai mata idon sai ta nai’imi da ya kawo mata kuɗi kimanin 500 inda shi kuma yace bashi da kuɗi saboda haka sai tace yaje ya ajje idon a wani guri in ya samu ƙudin sai ya kawo mata domin a gudanar da aikin.

Bayan yan sanda sun faɗada bincike a yanzu haka an cafke wanda ake zargi tare da wannan tsuhuwa, a yanzu haka a miƙa wannan lamari ga sashin binciken manyan laifuka na hukumar yan sandan jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!