Kar kayi gangancin bayarda umarnin a saki Nnamdi Kanu. ~Gamayyar ƙungiyar Arewa (CNG) ta gargaɗi Shugaba Buhari
Ƙungiyar gamayyar Arewacin Nigeria (CNG) ta ƙalubalanci kiraye-kirayen da ake akan Shugaba Muhammadu Buhari ya saki Shugaban ƴan tawayen kafa ƙasar Biafra wato Nnamdi Kanu.
A kwanakin baya ne dai Shuwagabannin yankin na Igbo suka ziyarci Shugaba Buhari a fadar Shugaban ƙasa tare da neman buƙatar ya sake shi. Yayin da Shugaba Buhari ya mayar musu da martanin cewa zai duba yiwuwar hakan.
A gefe guda ne kuma Ƙungiyar ta gamayyar ƴan Arewa ta suffanta neman buƙatar a saki Kanu a matsayin wani hari na ɗaukewa shari’ah hankali tayi abinda ya dace. Tare da cewa waɗanda suka nemi wannan buƙata ya kamata suma a hukunta su tare da masu ɗaukar nauyin Nnamdi Kanu yana cin zarafin bil-Adama da sunan neman ƴan-cin-kai.
Wannan yana ƙunshe cikin wani jawabi na musamman da mai magana da yawun ƙungiyar wato Abdul-Azeen Suleiman ya gabatar yayinda ake gudanar da taron ƙungiyar jiya Litinin a Jihar Kano. Ya kuma soki martanin da Buhari yayi ga Dattijawan yankin na Biafra a yayin ziyar, tare da ayyana cewa ƴan Arewa su zargi Buhari duk irin ta’addancin da Nnamdi Kanu ya sake haddasawa akayima ƴan uwansu bayan an sake.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta wallafa, Suleiman ya bayyana cewa kamar yadda suke cigaba da tattara binciken tsanaki kan aika-aikar da akayiwa ƴan Arewa a kudu maso Gabas, a yanzu sun gano cewa daga shekarar 2017 zuwa 2020 Kanu ya kitsa tare da umartar kashe aƙalla ƴan Arewa mutane 1,230 waɗanda suke zama a yankunan na Inyamurai, bayan kuma kayayyaki na miliyoyi da suka lalata mallakin ƴan kasuwar Arewa.
A karshe, ƙungiyar ta gargaɗi cewa Arewa ba zata sake zuba ido ana cin zarafin ƴan Arewa mazauna yankin Inyamurai ba, ya zama a rinƙa ɗaukar matakin daya dace.