Labaran Kannywood

Jaruma Hadiza Saima ta bayyana babban burinta a game da Yarta Surayya Salisu Yahaya

Jaruma Hadiza Saima ta bayyana babban burinta a game da Yarta Surayya Salisu Yahaya

Fitacciyar Jaruma a Masana’antar Kannywood Hadiza Muhammad, wacce akafi sani da Hadizan Saima, ta bayyana babban burin da ta ke da shi game da ‘yar ta Surayya Salisu Yahaya.

Hadiza ta bayyana burin ne a cikin hirar ta da mujallar Fim kan bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yar tata da aka yi a Kano.

A yanzu babban burin da na ke fata shi ne Allah ya nuna mani lokacin auren ta. Ina fatan Allah ya ba ta miji nagari, kuma Allah ya ƙara mana shekaru masu albarka cikin ƙooshin lafiya da kwanciyar hankali.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa jaruman Kannywood a yanzu duk girma ya kama su daga don haka a yanzu sun koma bikin ‘ya’ya da jikoki. A yanzu ko bikin zagayowar ranar haihuwa wasu jaruman sun daina yin nasu sai dai na ‘ya’yan, kamar yadda ya faru ga Hadizan Saima.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!