ABINDA BAKA SANI BA SANI BA AKAN INTERNET – Abdulrahman Master

ABINDA BAKA SANI BA SANI BA AKAN #INTERNET
Wannan rubutun nayi shi shekaru biyu da suka wuce amma har yanzu kamar al’umma basu hankalta ta #Internet ba. Yakamata mu gane ba kowane sirri ake bawa waya ko Computer ajiyarsa ba a wannan zamanin.
$. INTERNET
Kafin fara amfani da kowane sabon abu daya shafi wani bangare da bamu da iko a kansa ko muke da karancin sani yakamata muyi bincike kafin muyi amfani dashi ta kowanne bangare.
Abu ne mai girman gaske wanda har yanzu ko turawan da suka kirkireta basu san iyakar abinda take iyayi ba, kullum updating akeyi da upgrading sai abinda ka gani gwargwadon iya fahimtar ka da iliminka. Babu wani lungu da sako da #Internet bata da damar shiga domin sanin abinda ke wannan sashi. Idan akace #Internet nasan dayawa za suyi tunanin Browsing, Chatting da sauran wasu abubuwa kadan daga cikin abinda take iyayi.
Kamar yanzu yadda Internet tayi karfi, yazamana duniya bata da sirri duk wani abu da kakeyi kasa a ranka ana ganinka ko za’a iya ganinka ko jin abinda kakeyi a duk lokacin da aka ga dama idan har kana amfani da waya ko kuma akwai masu amfani da ita a kusa da inda kake.
Dayawan mutane suna amfani da wayoyin zamani (smart phones) ba tare da sun san gaskiyar abinda wayar ke iyayi akansu ba. Wasu kawai dan tana da kyau ko camera me kyau ko battery da sauransu. Wallahi akwai wayarda indai ka siyeta to har abada baka da sirri. Duk wani amfani da zakayi da ita a hannunsu yake, kamar Call, SMS, Chat, Pictures/Videos da sauransu. Duk abinda zakayi an sani.
Misali kamar applications, babu wata waya da zatayi aiki ba tare da application ba, akwai millions na application daban-daban a duniya sai wanda kayi niyyar amfani dashi. Abin lura game da apps shine suna da access getway ma’ana akwai wasu hanyoyi da suke samun bayanan cikin wayarka. Kowanne app yana da Terms and conditions idan ka karanta zaka gani.
Duk app din da kayi installing wanda babu shi akan wayar, da zarar ka bude zai nuna maka yana bukayar bayani daga wani bangare na wayarka. Misali WhatsApp zai ce maka WhatsApp want to access your contact sai kaga a kasa an nuna maka Allow or Deny, idan baka amince ba to wlh bazeyi ba ko me zaka masa.
Wadannan app din da muke amfani dasu sosai wajen chat kamar
Facebook
Twitter
Instagram
Whaysapp
Da sauransu,
Muna basu duk wasu baya nan mu ta hanyoyi kamar haka!
Camera
Cantact
Location
Phone (kira)
Calendar
Microphone
Gallery
Da sauransu.
Dukkan wadannan apps din zasu iya bada duk bayanan ka cikin sauki kuma duk wani abu da zakayi sun sani, baka da wani sirri idan kana tare dasu. Abubuwan dayawa, bazan iya fadar komai ba anan. Akwai bangare waya wannan dogon labari ne sai na zauna. Amma wlh bamu da sirri ko kadan matukar muna amfani da Smat phones.
Abdulrahman Master