Labaran Kannywood
Inna Lillahi! Mutuwar Mawaki Naziru Sarkin Waka Ta Jijjiga Duniya – Labarai.com.ng

Mawaki Naziru Sarkin Waka Ya Karyata Labarin Mutuwar Shi Da Ake Yadawa
Fitaccen jarumi kuma mawaki a cikin masana’antar Kannywood Naziru M Ahmad wanda wasu sukafi sani da Naziru Sarkin Waka ya Karyata labarin da ake yadawa akan shi na ya mutu.
Mutuwar Naziru Sarkin Waka |
Ya bayyana hakan a shafukan sada zumuntar sa irin su Facebook da kuna Instagram.
Jarumin ya bayyana kamar haka: “Saurin me kuke yi,Allah ya shirya ku yasa mudace Amin.”
Haka dai mutane sukaci gaba da bayyana ra’ayoyin su akan hakan.
Daman kuma idan baku manta ba a irin wannan lokacin ana yawan yada Labaran kanzon kurege na mutuwar manyan Jaruman Kannywood.
Allah yasa mu cika da imani Amin.
Www.labarai.com.ng