Hukumar tace Finafinai ta Jahar Kano ta Dakatar da Jaruma Khadija Mai Numfashi Sanadiyyar Wata rawar gala da tayi a Kasar Niger

Hukumar tace Finafinai ta Jahar Kano ta Dakatar da Jaruma Khadija Mai Numfashi Sanadiyyar Wata rawar gala da tayi a Kasar Niger
Abba Almustapha shine Shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, a satin da ya gabata ya dakátar da wani dan film dan daudu wanda suke kira Alin Kwana casa’in saboda abubuwan bat$a da i$kanc¡ da yake yadawa
Yau kuma sai muka sake cin karo da labarin cewa Abba Almustapha ya sake dakatar da wata ‘¥àr i$kà mai shirin fim wanda suke kira da sunan Khadija Mai Numfashi saboda tayi rawar bat$a
Abba Almustapha ya dakatar da wannan wakilan ¡bli$ na tsawon shekaru biyu daga shiga harkan fim, har ma naji yana cewa zai gurfanar da su a Kotu saboda sun kárya doka
Tsakani da Allah Abba Almustapha ya burgeni, ban taba tsammanin shi din mutumin kirki ne sosai kamar haka ba, domin har lokacin da aka bashi Shugabancin wannan hukuma sai da na kalubalanceshi, ashe dai zai yi abin a yaba
Tabbas idan aka cigaba da daukan irin wannan mataki da Abba Almustapha yake dauka za’a kawo sauyi mai ma’ana a masana’antar Hausa film