Abba Kyari
Hukumar NDLEA tana neman DCP Abba Kyari ruwa a jallo.

Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Nigeria ta bayyana tsohon ma’aikacin ɗan Sanda Abba Kyari a matayin wanda take nema ruwa a jallo.
Wannan ya fito ne a yau Litinin, ta hannun mai magana da yawun hukumar.
Ya kuma bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja.