EFCC

Hukumar EFCC ta cafke wasu mutane da ake zargi da almundahana ɗauke da katin ATM aƙalla 1,144 a Jihar Kano.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta cika hannu da wasu mutane a Kano bayan kamasu da katin ATM sama da dubu ɗaya.

Wilson Uwajaren mai magana da yawun Kwamishin nan na EFCC a Jihar Kano shine ya bayyana haka, tare da bayyana cewa an kama mutanen tun ranar 24 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba 2021.

Mutanen da ake zargi da wannan almundahana sun haɗa da Abdullahi Usman, Musa Abubakar da kuma Abdulwahid Auwalu.

A nasa ɓangaren, Musa Abubakar an kama shi ne yayin da yake ƙoƙarin tafiya Dubai ɗauke da katin ATM akalla 714 tare da shi.

Abdulwahid kuma yana ƙoƙarin tafiya Saudi Arabia ɗauke da katin ATM 298. 

An bayyana cewa za’a gurfanar da su a gaban Kotu domin binciken ƙwaƙwaf dangane da lamarin.

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!