Uncategorized

Haramun ne shiga gasar kyawawa a Musulince. ~Cewar MURIC

Ƙungiyar kare haƙƙoƙin Musulmi a Nigeria, [MURIC] ta bayyana goyon bayanta ƙarara bisa ga matakin da hukumar Hisba ta ɗauka na gayyatar iyayen Shatu Garko zuwa ofishinsu bayan da matashiyar ta lashe kanbun Sarauniyar Kyawu ta Nigeria a wannan karon.
Babban daraktan Ƙungiyar mai suna Farfesa Ishaq Akintola cikin wata tattaunawa da Jaridar Punch, ya bayyana cewa babban kuskure ne ga Musulmi mace ko namiji ya shiga gasar kyawu, tare da ƙarin cewa babu bambanci tsakanin shiga gasar kyawu da wasan kwaikwayon BBNaija da ake gabatarwa a kudancin Nigeria.
A safiyar yau ne dai babban Kwamandan Hisba mai suna Haroun Ibn Sina ya aike da takardar gayyata ga iyayen Shatu Garko, bisa ga matakin da yarinyar ta ɗauka na shiga gasar kyawawa ta ƙasa, wanda a cewar Ibn Sina yin hakan haramun ne a Musulunce.
Har’ilayau, Farfesa Akintola ƙara da cewa, ba ayiwa Musulmi umarni akan su shiga gasar kyawu kowacce iri ba. Kamar yadda aka saukar cikin Al-Qur’ani.
A bisa wannan dalilan ne, Farfesan ya bayyana cewa duk Musulmin ƙwarai bai kamata yayi farin ciki da abinda Shatu Garto tayi ba.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!