Uncategorized

Hanyoyin Shiga Aljannah Guda 30|Arewaaga.com.ng

HANYOYIN SHIGA ALJANNAH 30

Wadannan Hadisai duk sun tabbata daga Manzon Allah s.a.w, duk wanda ka dauka zai kaika/ki aljannah:-
.
¤1- Manzon Allah s.a.w yace:-“duk wanda yayi sallolin asuba da la’asar akan lokaci, zai shiga ALJANNAH”
.
¤2- Duk wanda ya rike karanta AYATUL KURSIYYU bayan ko wacce sallah, babu abinda zai hanashi shiga ALJANNAH face mutuwa”
.
¤3- Duk wanda yake karanta suratul MULK kafin ya kwanta bacci, zata cece shi zuwa ALJANNAH”
.
¤4- Duk wanda yayi ALWALA sannan ya kyautata alwalar, sannan bayan ya gama yace:- ASH HADU ALLA’ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKALAH, WA ASH HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WARASULUH’ za’a bude masa kofofin ALJANNAH guda takwas, ya zabi ta wacce zai shiga”
.
¤5- Duk wanda yayi sallolin NAFILA goma sha biyu a dare da yini, Allah zai gina masa gida a ALJANNAH”
.
¤6- Akwai wata kofa a ALJANNAH mai suna ARRAIYAN, babu mai shiga ta wannan kofa sai masu yawan AZUMI”
.
¤7- Manzon Allah s.a.w yace yaga wani mutum yana yawo a cikin gidan ALJANNAH saboda wata BISHIYA daya sareta akan hanya kada ta cutarda mutane”
.
¤8- Duk wanda ya riki GASKIYA a maganganun sa, zata shiryar dashi zuwa ALJANNAH”
.
¤9- Duk wanda ya kiyaye HARSHEN sa da AL’AURAR sa, Annabi s.a.w yace shi kuma ya lamunce maka ALJANNAH”
.
¤10- Manzon Allah s.a.w ya gayawa sahabinsa kada kake yawaita FUSHI zaka shiga ALJANNAH”
.
¤11- Duk wanda yaje duba MARAR LAFIYA, zai shiga ALJANNAH”
.
¤12- Allah s.w.t Ya fadi a Hadisin kudsi, duk wanda BALA’I yazo masa, karon farko yayi HAKURI, babu abinda ya dace dashi face ALJANNAH”
.
¤13- Duk MACEN da ta sallaci SALLOLINTA biyar, ta AZUMCI watanta, ta kiyaye FARJINTA, tayi biyayya wa MIJINTA, zata shiga ALJANNAR ubangijinta”
.
¤14- Manzon Allah s.a.w yace, duk wanda ya lamunce min bazaiyi ROKO ba, zan lamunce masa ALJANNAH”
.
¤15- Wanda yayi LADANCIN shekara 12 zai shiga ALJANNAH”
.
¤16- Duk wanda a kokarin kare DUKIYARSA aka kashe shi, zai shiga ALJANNAH”
.
¤17- Duk wanda ya toshe wata kofa, a sahun JIHADI ko SALLAH, ALJANNAH ta tabbata gareshi”
.
¤18- Babu wanda zai MUTU bashida GIRMAN KAI, HA’INCI, BASHI face ya shiga ALJANNAH”
.
¤19- KUNYA na cikin IMANI, Imani na ALJANNAH”
.
¤20- Manzon Allah s.a.w yace duk wanda y lamunce masa abubuwa guda 6, shi kuma zai lamunce maka ALJANNAH! Duk maganan da zakayi ka fadi GASKIYA, ka cika ALKAWARI idan ka dauka, ka bayarda AMANA idan an amince maka, ka kiyaye FARJINKA, ka rintse IDANUNKA daga kallon haram, ka rike HANNAYENKA daga zalunci”
.
¤21- Duk wanda ya kewa Iyayensa BIYAYYA zai shiga ALJANNAH”
.
¤22- Duk wanda ya kasance mai yawan ALWALA, kuma idan yayi saiya mata NAFILA zai shiga ALJANNAH”
.
¤23- Duk wanda ya SHAIDA da kalmar SHAHADA, ya shaida Annabi Isa a.s bawan Allah ne, kuma Aljannah gaskiyace, Wuta ma gaskiya ce, Allah zai shigar dashi ALJANNAH gwargwadon aikin shi”
.
¤24- Duk wanda ya zamto mai daukan nauyin MARAYA, zai kasance tareda Annabi s.a.w a ALJANNAH”
.
¤25- Duk mai saukin kai wajen saye da sayarwan sa, Allah zai shiryar dashi ALJANNAH”
.
¤26- Duk ALKALIN da yasan GASKIYA yayi aiki da ita, zai shiga ALJANNAH”
……………………………………….
*******************
Wadannan kuma bacin yan Aljannah ne kuma Shahidaine:-
¤27- Duk wanda gini ya fado masa ya MUTU”
.
¤28- Duk wanda CIWON CIKI ya kashe shi”
.
¤29- Duk wanda ANNOBA tayi ajalinsa”
.
¤30- Duk wanda ya nitse RUWA ya zamo ajalinsa”
★★★★★★★★★★★★★★★
Dafatan Allah Ya bamu ikon aikinda zamu shiga aljannah Allahumma Amin
Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!