Uncategorized

Gwamnatin tarayya ba ta da kuɗaɗen da zata biya buƙatun ASUU. ~Cewar Christ Ngige

Ministan ƙwadago na ƙasa, Dr Christ Ngige ya bayyana cewa Gwamnatin Nigeria ba ta da kuɗin da zata biya ƙungiyar ASUU buƙatunsu.

Ngige ya bayyana hakan ne a jiya yayin wata tattaunawa ta musamman da shafin TV Channel.

Ya bayyana cewa sun zauna da ƙungiyar malaman Jami’o’i ta ƙasa kuma sun saurari kokensu, amma ba su da halin biya musu buƙata a halin yanzu.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne dai ƙungiyar ASUU ta shiga yajin aikin wata ɗaya sakamakon gaza cika alƙawuran da Gwamnatin tarayya tayi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!