Labaran Duniya

Gwamnati tarayya ta shawarci yan Nigeria mazauna Ukraine akan su kula da kansu.

Gwamnatin tarayya ta shawarci ƴan Nigeria mazauna Ukraine akan su kula da kansu.

Bayanin ya fito ne ayau daga ofishin Jakadancin Nigeria a ƙasar ta Ukraine. Inda wakilin Nigeria a Ukraine ya shawarci ƴan Nigeria mazauna can akan su kula da kansu a yayinda aka fara gwabza yaƙi tsakanin Russia da Ukraine.

Dubunnan ƴan Nigeria ne suke zaune a ƙasar ta Ukraine waɗanda mafi yawansu karatu suke yi a jami’o’i daban-daban.

Da safiyar wannan rana ne kasar Rasha ta fara atisayen kai hari a wani yanki na Ukraine, al’amarin da ya fara ɗaukar hankalin ƙasashen Duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!