Uncategorized

Gwamnan Jihar Ondo ya ce wajibi Shugabancin Nigeria ya koma kudu a 2023.

 Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo bayyana cewa ya zama wajibi Shugaban ƙasar Nigeria a karo na gaba ya fito daga yankin kudu.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi na musamman a taron da Jami’ar Obafemi Owolowo ta shirya karo na 45.

Akeredolu ya ce, “kowanne sashi na al’umma ya kamata su shiga a dama dasu a al’amuran ƙasa, kuma babu yankin da ya kamata a ware a gefe; don haka a 2023 dole ne madafun iko su koma kudancin Nigeria.

Nigeria ba zata kai ga nasara ba, musamman duba da yadda al’amura suka taɓarɓare a halin yanzu.

Ko da yake, Akeredolu yayi jawabin cewa yana da yaƙinin Nigeria zata dawo da martabarta duk da rashin cigaban da kullum ake fuskanta ta fanni daban-daban.

Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki a daga sassan Nigeria, waɗanda suka haɗa da; muƙaddashin Shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Gwamnan Jihar Osun, Adedboyega Oyetola da kuma Oonin Ille-ife, wato Oba Adeyeye Enitan.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!