Uncategorized

Gwamna Zulum zai gudanar da bikin ƙaddamar da manya-manyan ayyuka guda 23 daya shimfiɗawa talakawa a Kudancin Jihar Borno.

 

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum yana yankin Kudancin Jihar Borno domin bakin buɗe ayyuka 23 da suka haɗa da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya a ƙauyuka daban-daban dake yankin.

A jiya Laraba, Gwamnan ya fara ƙaddamar da ayyukan daga ƙauyan Bayo.

Mai-magana da yawun Gwamna Zulum wato Malam Isa Gusau shine ya bayyana hakan.

Malam Gusau ya ƙara da cewa, “cikin ayyuka 22 da Zulum zai ƙaddamar, sun haɗa da sababbin makarantun Firamare da Sakandire guda 13, sai cibiyoyin kiwon lafiya guda 6, tare da ofishin ƴan sanda guda 1.

An kuma shinfiɗa ayyukan a ƙauyukan da suka haɗa da, Hawul, Shani, Bayo da kuma ƙaramar hukumar Kwaya Kusar dake yankin na kudancin Jihar ta Borno.

Har’ilyau; Isah Gusau ya tabbatarda cewa, cikin shekaru biyu, Gwamna Zulum ya kammala ayyuka aƙalla 556 a faɗin Jihar ta Borno.

Daya daga cikin muƙasudin tafiyar ta Zulum shine domin ganawa da Jami’an tare da ƙara basu ƙwarin gwiwar cigaba da tabbatarda tsaro a yankin na Kudancin Jihar Borno.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!