Labarai

Gwamna Wike ya baiwa wani Gurgu da ya kammala digirin-digirgir kyautar miliyan 50 tare da gurbin aiki a Jami’ar Jihar Rivers.

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya karrama wani gajiyayyen ɗalibi (gurgu) mai suna James E. Daniel da kyautar miliyan 50 tare da gurbin aiki a Jami’ar Jihar Rivers bayan da matashin ya kammala karatun digirin-digirgir a fannin Philosophy.

Gwamnan ya kuma gargaɗi Jami’o’i a faɗin Jihar ta Rivers akan su gujewa nuna banbanci wajen baiwa waɗanda suka cancanta sakamakonsu na digiri.

Gwamman ya miƙa kyautar ga wannan gurgu ne a jiya Asabar yayin taro na 33 da Jami’ar Jihar Rivers din ta gudanar a garin Fatakwal.

Wike ya ce, karramawar da akayiwa Dr Daniel tana da alaƙa da irin namijin ƙoƙarinsa a yayin da yake karatu a Jami’a tare da duba da yanayinsa na rashin lafiya amma hakan bai sanya shi ya rasa ƙwazon yin karatu ba.

 

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!