Labarai/Addini
Gwamna Matawalle ya bayarda gudunmawar miliyan 85 domin a gudanar da Mauludin Inyass a Zamfara.

Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin Dakta Bello Matawalle ta bayarda gudunmawar kuɗi naira miliyan 85 domin gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 14, wanda ake shirin gudanarwa a Jihar.
Wannan ya fito ne cikin wata takarda ta musamman wadda ta fito daga babban ofishin Gwamnatin Jihar ta Zamfara.