Makarantu

Gwamna El-Rufai ya kori Malaman makaranta 233 sakamakon gano su da takardun boge.

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori Malaman makaranta 233 sakamakon gano su da amfani da takardun boge tun loƙacin da aka ɗauke su aiki.

Tijjani Abdullahi, Shugaban harkokin ilimin farko a Jihar ta Kaduna shine ya bayyana haka a yau Alhamis yayin ganawa da manema labaru a garin Kaduna.

Ya bayyana cewa Malaman da aka kora, an kore su ne sakamakon yin amfani da takardun boge.

Ƙudirin na yin binciken ƙwaƙwaf ga Malaman ya fara aiki tun a watan Afrilu na wannan shekarar, wanda ƙungiyar aka bijoro dashi ƙarƙashin umarnin Gwamnatin Ƙaduna domin gyara ɓangaren na ilimi a faɗin Jihar.

A cewarsa, babban muƙasudin yin hakan shine domin a tabbatar cewa duk Malaman da aka ɗauka a matsayin ma’aikata domin koyarwa ya zamanta suna da cancanta tare da sahihan takardun makaranta.

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!