Tsaro

Gwamna Bello Matawalle ya sake bayarda umarnin rufe gidan Mai tare da gidan Biredi a Jihar Zamfara bisa zargin siyarwa da ƴan Bindiga abubuwa a sirrance.

 

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayarda umarnin gidan man-fetur da biredi a Jihar bayan zarginsu da taimakawa ƴan Bindiga a ɓoye.

Kwamitin ƙungiyar jami’an sakai sune suka shigar da ƙorafin hakan bayan kama mutane huɗu suna kaiwa ƴan Bindigar man-fetur tare da biredi ta ɓarauniyar hanya.

Mista Dauran, mataimaki na musamman ga al’amuran tsaro a Jihar Zamfara ya bayyana cewa, “za’a a rufe wani gidan Mai da yake ƙauyen Tsafe a ƙaramar hukumar Tsafe tare da wani gidan Biredi a Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara bayan zarginsu da siyarwa da ƴan bindiga kayayyakin a ɓoye.

Mutanen da ake zargi da sayarwa ƴan Bindiga Fetur da Biredi, an kama sune bayan ɗaukar loƙaci ana fakon su a sirrance. Wasu an kama su suna amfani da Galon, Jarka wajen kaiwa ƴan bindigar fetur.

Ya kuma bayyana takaicinsa da cewa, “duk da irin ƙoƙarin da Gwamnan Jihar ta Zamfara Bello Matawalle yake na ganin an shawo kan matsalar tsaro, a gefe guda kuma ga wasu marasa kishin ƙasa suna daƙile wannan buri.

A ƙarshe, Mista Maidan wanda shine mataimaki na musamman ga Gwamna Matawalle ta fannin tsaro ya buƙaci Kwamitin na ƙungiyoyin sakai, akan su cigaba da baiwa Gwamnati haɗin kai domin a samu nasarar shawo kan matsakar tsaro a Jihar Zamfara.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!