Labaran Duniya
Ganduje ya halarci taron sulhu a Abuja, bayan APC taƙi amincewa da Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar a Kano.

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya halarci tattaunawar da sulhu da ɓangaren su Shekarau bayanda uwar Jami’iyya taƙi amincewa da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar reshen Jihar Kano.
Gwamman ya halarci wurin tattaunawar tare ne, bayan da shugaban kula da ayyukan Jam’iyyar ta APC mai-mulki, Mai Mala Buni ya kira taron gaggauwa bayan rikice-rikicen Jam’iyyar da yayi ta ruruwa a Jihar Kano.
Har’ilayau, zaman ya tabbata ne, biyo bayan da uwar-Jam’iyyar ta APC mai helkwata a Abuja taƙi amincewa da Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen Shugaban Jam’iyyar a Kano.
Wasu daga cikin mahalarta taron, sun haɗa da, Mai Mala Buni, Sanata Kabiru Gaya, Barau Jibrin, Shaaban Sharada, Sanata Shekarau da kuma Alhassan Ado Doguwa.