Labarai
Fafaroma yayi kakkausar suka ga ma’auratan da basa son haifuwar yara.

Babban Shugaba a ɓangaren addinin Kiristanci mai shekaru 85 wato Pope Francis yayi kakkausar suka ga ma’aurata waɗanda ba su son haifar yara da yawa.
Pope ya bayyana haka ne gaban dubun-dubatar mabiya addinin Kirista a wannan taro a musamman da ya gaba a Vatican wato Rome dake Italiya.
Ya bayyana cewa, da yawan ma’aurata ba su son Iyali, amma a mainakon haka suna iya ajiye karnuka da maguna a gidajensu.
Ya kuma ƙara da cewa, “babu babbar wayewa ga ma’aurata fiye da samun iyali. Dalilin haka dole ma’aurata da suka yi aure musamman waɗanda basu son haihuwa su sauya tunani.
[email protected]