Labarai

Duk Mijin Daya Saki Matar Da Muka Aura Masa Haka Kurum, to Saiya Biya Gwamnati Kuɗin data Kashe Masa, Cewar Sheikh Aminu Daurawa

Duk Mijin Daya Saki Matar Da Muka Aura Masa Haka Kurum, to Saiya Biya Gwamnati Kuɗin data Kashe Masa, Cewar Sheikh Aminu Daurawa

Hukumar Hisba dake jihar Kano ta bayyana cewa za ta daura wa mata 1,800 aure sannan za ta yi wa mata kayan gara na daki.

Kwamandan rundunar Hisba ta Kano Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa hukumar za ta aurar da mata 1800 a Kano nan ba da dadewa ba.

Daurawa ya sanar da haka yayin da yake duba kayan ɗaki da aka yi wa matan a ranar Laraba a garin Kano.

Daurawa ya ce gwamnati ta ware naira miliyan 800 domin siya wa amaren kayan ɗaki.

“Kowace mace za ta samu setin gado, katifa, fulo da jarin naira 20,000.

“Wasu attajirai a jihar sun yi alkawarin bada nasu gudunmawar domin tallafa wa matan.

Daurawa ya ce nan ba da dadewa ba Hisba za ta sanar da ranar da za a yi bukin ɗaurin auren.

A Karshe Daurawa ya ce duk mijin da ya saki matar sa haka kawai kan abin da bai taka kara ya karya ba zai biya gwamnati kudin auren da aka kashe masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!