Davido Birthday

Davido YA SAMU ₦60 MILLION A RANAR BIRTHDAY DIN SA

 DAVIDO YA SAMU ₦60 MILLION A RANAR BIRTHDAY DIN SA.

Dazun nan a Tuwita, ina cikin shawagi na, sai nake duba wajen searching sai nake ganin Trending na Davido a under Nigeria, nace dai bari na leka dana shiga sai nake ganin abubuwan mamaki, kamar al mara sai kawai na basar domin manyan influencers na duniya suna yin irin haka, wasu na fundraising ko kuma irin Donations da suke yi na kungiyoyi.

Tweet na farko dana gani shine na Davido din kansa, in da naga ya wallafa cewa “If u know I’ve given you a hit song .. send me money …. una know una selves oo 😂😂😂🥰🥰🎉🎉” fassara, idan kasan nai maka waƙa me dadi to ka turo mun kuɗi…

A Tweet na biyu kuma ya ajiye wema Bank account din sa, domin ta nan za’a tura masa kudin, jama’a mutanen sa sun amsa kiran kuma sun tura, kamar yanda ya sake yin Tweet na uku aciki yake fadin cewa a cikin mintuna 10, an tura masa da 7 million.

Jumullar abunda aka saka masa zuwa sanda nake wannan sharhin shine, miliyan 67, da dubu 539, da dari 909, da ɗigo 75 (₦67,539,909.75). 

————————

Darasin da zamu dauka.

————————

Abu na farko dai shine Ni zan iya cewa, wannan abin da mawakin Davido yayi Ni Banga aibun sa ko laifin sa ba, kuma ya cancanci hakan, domin ya budewa abokan sa kofofin samun alkhairi bi ma’ana sila, kuma ya taimaki wasunsu da dama.

Abu na biyu kuma shine, yanzu muna lokaci ne da zakai investing akanka kuma kaci riba, me hakan yake nufi? Maslan shi Davido a bangaren sa na waka , nasan cewa akwai wakokin da yayi wanda bai samu return na profit ba, kudin sa da rancen abokai zai je studio a naɗa ya fito da ita domin ya nishadantar da masoyansa.

Abu na uku kuma shine, girmama Community din dake Following nasa, me nake nufi shine, davido yayi investing again akan su kansu mabiyansa na shafukan sada zumunta, ta hanyar basu nishadin da zasu kasance tare a matsayin followers nashi. Shin kai ma kana investing irin wannan kuwa? ana yi, kuma gashi kaga yanda yake amfani.

Mustapha Gfatu ✍️

(Dan Fafutukar yaki da Kinko)

Www.labarai.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!