Labarai
Dattawan Jihar Katsina sun kaiwa Buhari kokensu dangane da rashin tsaro a Katsina.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da dattawana Jihar Katsina wanda Gwamna Bello Masari ya jagoranta yau Talata a fadar Shugaban ƙasa dake Abuja.
Gwamna Masari shine ya jagoranci tawagar, yayinda suka tattauna da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a sirrance bisa ga al’amuran da suka shafi tsaro.
Dattawan sun haɗa da; Sanata Abba Ali, Alhaji Aliyu Mohammed, Sanata Mamman A. Danmusa, Alhaji Nalado Y. Sarkin Sudan da kuma Alhaji Ahmed Yusuf.
Www.labarai.com.ng