Labaran Duniya

Dan Marigayi Mu’ammar Gaddafi Ya Fito Takarar Shugaban kasar Libya – Labarai.com.ng

 Dan marigayi tsohon Shugaban kasar Libya Mu’ammar Gaddafi mai suna Saif al-Islam ya yi rajistar tsayawa takarar shugaban ƙasar Libya a zaɓen watan Disamba mai zuwa, a cewar labarin hukumar zaɓen ƙasar ta Libya.


“Saif al-Islam ya miƙa rajistar takararsa ta shugabancin ƙasa zuwa ga hukumar zaɓe a birnin Sebha,” in ji hukumar.


Ta ce ya cika “dukkan ƙa’idojin da ake buƙata” sannan kuma an ba shi katin jefa ƙuri’a na gundumar Sebha nan take.


Wannan ne karon farko da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a matakin gama-gari a Libya ranar 24 ga Disamba na wannan shekarar ta 2021 bayan Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta shiga tsakanin ɓangarorin da ke yaƙar juna a ƙasar.


Labarin ya mutakar burge mutane,Amma sai dai wasu suna ganin kamar hakan ya bar baya da kura.


Shin mene ra’ayin ku game da takarar Dan tsohon Shugaban kasar Library din Saif?

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!