Da Dumi-Dumi Zainab Indomie Ta Dawo Kannywood

Zainab Indomie fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood tayi batan dabo a shekarun baya inda aka neme ta aka rasa a lokaci daya.
Sai dai a yau 25 ga watan Junairun shekarar 2022 an gano jarumar tare da abokin aikin ta jarumi Adam A Zango tare wajen daukar sabon shirin kamfanin Prince Zango Production mai suna “Asin Da Asin”.
An gano jarumar ne sanye da rigar tallar fim din da ake dauka ne a lokacin a cikin wani dakin hotel da suke gudanar da daukar ayyukan fim din, jarumar ta bayyana ne suna tikar rawa na wata wakar Jarumin Adamu Zango.
Tun bayan bayyanar bidiyon mutane da dama suke ta yama didi dashi,a yayin da wasu kuma daga gefe guda suke taya Indomie din fatan nasara da dawowa cikin Sa’a.
Shin mene fatan ku akan jarumar Zainab Indomie din?
Shin kuna ganin dawowarta zata cigaba da gashi daga inda ta tsaya kamar yadda take a baya?
Muna dakon amsoshin ku.
Zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa 👇👇👇