Uncategorized
Cire tallafin man-fetur zai haɓɓaka harkokin kasuwancu a Nigeria. ~Cewar masana ta fannin Kasuwanci

Babban manajan darakto, George Onafowokan ya bayyana cewa cire tallafin man-fetur zai haifar da alkhairi game da al’amuran kasuwanci da kuma tattalin arziƙi a Nigeria.
Mista George, ya bayyana haka ne a jiya, Asabar yayin tattaunawa da manema labarai dangane da lamarin na janye tallafin man-fetur.
Ya bayyana cewa, “yafi alkhairi a kashe biliyoyin kuɗaɗen da ake kashewa domin gina masana’antu fiye da bayar da tallafin man-fetur.
Akwai hanyoyin da ya kamata a yi amfani da kuɗaɗen wanda hakan zai iya kawo sauyi a tattalin arziƙin Nigeria.