Labarai

Buhari ya cancanci yabo bisa ƙoƙarin magance matsalar tsaro da yake a Nigeria. ~Inji Garba Shehu

Mai-magana da yawun Shugaban ƙasa wato Malam Garba Shehu ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya cancanci yabo bisa ga namijin ƙoƙarin da yake wajen shawo kan matsalar tsaro tare da rikici tsakanin manoma da makiyaya a Nigeria.

Ya bayyana haka ne ayau Juma’a yayin wani biki na musamman da Jami’ar tarayya dake Dutsin-Ma (FUDMA) ta shirya game da illar yaɗa labaran ƙarya tare da matsalolin da suke fuskantar ɓangaren.

Malam Garba Shehu ya ce, “maganar gaskiya Gwamnatin Shugaba Buhari tana ƙoƙari a ɓangaren tsaro, kamar yadda aka samu nasarar shawo kan faɗace-faɗace tsakanin manoma da makiyaya rikicin daya samo asali tun bayan samun ƴancin Kai.

Sannan rikice-rikicen kaɓilanci da addini tare da irin matsalar tsaro da aka shiga sune manya-manyan ƙalubalen da Gwamnatin Buhari ta sanya a gaba domin magancewa. Amma kuskure ne mutane suyi iƙirarin cewa wai Gwamnati bata ƙoƙari a waɗannan ɓangarorin.

Har’ilayau, Shehu ya ƙara da cewa, kamar yadda ake samun nasarori ta fannin yaƙi da ta’addanci; akwai buƙatar a samu haɗin kan Gwamnoni tare da gama-garin mutane domin a cimma abinda ake so.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!