Labarai

Buhari ya bayyana cewa yayi iyakar abinda zai iya, kuma yana fatan ƴan Nigeria za su fahimci haka ko bayan barinsa ofis.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayi iyakar abinda zai iya, kuma yana fatan ƴan Nigeria za su fahimci haka ko bayan barinsa ofis.

Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayi tattaunawa da gidan Telabijin na NTA.

Shugaba Buhari zai ƙarƙare mulkinsa a shekarar 2023, yayinda yake ta cigaba da fuskantar ƙorafe-ƙorafen ƴan Nigeria sakamakon gazawarsa ta ɓangaren tsaro, tattalin arziƙi da sauran cigaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa “na bayarda dukkan irin gudunmawar da zan bayar, kuma ina fatan ko bayan bana kan mulki ƴan Nigeria za su gasgata haka.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Buhari ya rufe da cewa “bana buƙatar godiya daga ƴan Nigeria, buri na kawai su fahimci cewa nayi iyakar ƙoƙari na.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!