Buhari Ka Gaza Ka Sauka Kawai – Jaruman Kannywood
Tun bayan da aka kone matafiya guda 42 a jihar Sokoto a cikin motocin su. Mutane da dama sunyi Allah wadai da hakan data faru,ba’a bar jaruman Kannywood a baya ba domin kuwa jarumi Ali Nuhu da sauran jaruman Kannywood din sunyi Allah wadai da al’amarin daya faru.
Jarumi Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa kamar haka:
“Ya kamata wadanda suka mutu a motar da aka kona a sokoto su ma a yi wannan binciken a dau mataki akan daukar ran su da aka yi ba gaira ba dalili.”
Falalu A Dorayi ya bayyana a shafinsa kamar haka:
“Ana maganar rayuka sun salwanta ciki hadda na Jarirai, Shugabanni sama na shirin Kaddamar da littafin Bisi Akande.
Akande da littafinsa, sunfi Mutanen da aka KONE kenan.
Na dauka in masifa ta faru, ta cigaba faruwa, Jagorori ajjiye komai suke suyi aiki tukuru wajan ganin sun kawo karshenta ko rage mata karfi.
Ko da yake ba abin mamaki ba ne, Jagororinmu sai kana da muhimmanci suke zuwa inda kake, duk kuwa da irin azabar da kake sha gun ‘Yan Ta’adda
Duk tsayin GONA dai akwai KUNYAR karshe.
(2023)”
Jaruma Samira kuma ta wallafa kamar haka:
Haka dai jaruman ba adadi suka cigaba da bayyana alhinin su akan abunda ya faru.