Tsaro
Trending

Bello Turji ya bayarda umarnin a saki mutane 52 da akayi garkuwa da su ba tare da biyan ko sisi ba.

Shahararren shugaban ƴan ta’adda mai suna Bello Turji, ya bayarda umarnin a saki mutane 52 waɗanda suke tsare a hannunsu tsawon loƙaci.

Umarnin ya tabbata ne, biyo bayan wani umarnin kai tsaye da Bello Turjin ya bayar da safiyar yau Litinin.

Turji, shine mutumin da ya ɗauki dogon loƙaci yana jagorantar ta’addanci, satar shanu da ayyukan garkuwa da mutane a yankunan Shinkafi da Sabon Birni dake Jihar Zamfara.

Har’ilayau; wasu kafofin sun wallafa cewar sallamar mutanen dai yana ƙunshe cikin wata yarjejeniya tsakanin Dakarun Sojoji da ƴan bindigar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!