Labarai

BABBAR MAGANA: Wani Matashi Zai Siyar Da Kansa a Kano Saboda Tsananin Talauci da yake fama dashi – Labarai.com.ng

BABBAR MAGANA: Wani Matashi Zai Siyar Da Kansa a Kano Saboda Tsananin Talauci da yake fama dashi.
Wani matashi mai suna Aliyu Idris Wanda wasu zasu iya sanin bidiyonshi a shafin TikTok, ya bayyana cewa a shirye yake ya siyar da kansa saboda tsanin da yake ciki na talauci.
Matashin wanda ke ɗauke da wani kwali a kan titin gidan Zoo dake Kano da rubutun “Wannan mutumin na siyarwa ne” ya ja hankalin mutane da dama dake wucewa.
Aliyu ya bayyana cewa halin ƙunci da matsin rayuwa ne ya sanya shi yanke shawarra siyar da kannasa domin samun mafita.
Matashin ya fada kamar haka:
“Duk wanda ya siye ne, za mu je ayi shi a rubuce na siyar da kaina, a kirawo yan’uwana suma za su yarda na siyar da kaina saboda suna cikin ƙuncin talauci.” Inji shi
Matashin ya bayyana cewa duk wanda ke shirin siyansa zai iya tuntuɓarsa ta lambar wayarsa.
”Ga lambata ga duk mai son siyana, 08140402192″.
Matsin tattalin arziki dai da ake ciki a wannan ƙasa ya jefa mutane da dama cikin mawuyancin hali.
Allah ya kawo mishi mafita Amin.

 

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!