Uncategorized

Babban bankin ƙasa CBN yayi gargaɗin wallafa sunayen manoman da suka karɓi rance domin noma da kiwo kuma suka hana, tare da hukuncin shekaru biyar a gidan yari.

 Babban bankin ƙasa CBN ya bayyana cewa yana gaff da wallafa sunayen mutanen da suka cinye kuɗin shirin noma da kiwo wanda Gwamnati ta gudanar a Shekarun baya.

Sun kuma gargaɗi cewa duk wadanda suka ranci kuɗaɗenn noma kuma suka ƙi biya, za su iya fuskantar hukuncin shekaru biyar a gidan yari.

A cewar CBN, tun da farko an tsara bayarda rancen kuɗaɗen ne domin haɓɓaka harkokin noma da kiwo, amma wasu suka ƙyanƙyashe suka ƙi dawo da kuɗaɗen.

Hakazalika, babban bankin yayi alƙawarin ɗaukar matakai akan mutanen da suka bijirewa tsarin tare da ganin an tabbatarda dawo da kuɗaɗen kamar yadda kowa ya karɓa.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!