Labaran Duniya

Ba za’a cire tallafin man-fetur a halin yanzu ba. ~Cewar Ahmed Lawan

Shugaban majalisar dokoki ta ƙasa Ahmed Lawan ya alƙawartawa ƴan Nigeria cewa Gwamnati baza ta cire tallafin man-fetur a halin yanzu ba.

Lawan bayyana haka ne yayinda yake amsa tambayar ƴan jaridu jim kaɗan bayan ganawar sirri da yayi da Shugaba Muhammadu Buhari.

A cewarsa, a halin yanzu Shugaba Buhari bai umarci kowa domin a cire tallafin man-fetur ba, kamar dai yadda ake ta harsashe.

Ya kuma bayyana cewa, tabbas ƴan Nigeria za suyi farin cikin cewa na gana da Shugaban ƙasa bayan mun tattauna akan batutuwa daban-daban, a ƙarshe ya alƙawarta na sanarwa da al’umma cewa babu sauran batun cire tallafin man-fetur a halin yanzu.

A ƙarshe, Ahmed Lawan ya bayyana cewa mun san yadda ƴan Nigeria suka damu game da zancen cire tallafin man-fetur, kuma babu maganar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!