Labaran Kannywood
Auren Jaruma Zarah Diamond ya mutu yayin da Mai Shadda yana shirin Wuf da Hassana Muhammad

Auren fitacciyar jarumar nan ta Kannywood wadda tayi shura a Shekarar da mukayi ban kwana da ita wato Zarah Diamond ya mutu,bayan kasancewa a gidan Mijinta na tsawon watanni da basu wuce biyar ba,haka zalika daman mutane na fadin cewa basu fiya Zaman aure ba domin yayi wuya kaga sun shekara a gidan mazajen nasu.
Zarah Diamond ta fito a cikin finafinan masu girma kana ta fito a cikin wani shirin kamfanin FKD kafin shigar ta gidan miji.
Su kuwa Abubakar Bashir Mai Shadda tare da Hassana Muhammad tuni hotuna sukayi nisa ana saka ran a satin nan mai zuwa zasu angwance,Allah ya basu zaman lafiya.