Labaran Kannywood

Auren Aisha Tsamiya Ya Mutu,dalilin rabuwar su da mijin…

AUREN fitacciyar jarumar Kannywood A’isha Aliyu Tsamiya ya daɗe da mutuwa, a binciken da mujallar Fim ta yi.

 

Mutane sun daɗe su na raɗe-raɗi kan idan auren ya mutu ne saboda irin hotunan da ake ganin ta na sakawa a TikTok masu nuna kamar ita ba matar aure ba ce; yadda ta ke saka sautin waƙoƙin Kannywood, ta na bi ta na rerawa ya haifar da kokwanto game da matsayin auren nata.

 

 

Binciken da mujallar Fim ta yi a ‘yan kwanakin nan ya tabbatar da mutuwar auren.

 

Wata majiya mai tushe ta kurkusa da jarumar ta shaida mana cewa auren ya mutu tun a watanni uku zuwa huɗu da su ka gabata.

 

Majiyar ta ƙara da cewa mutuwar auren “ba wani abin mamaki ba ne saboda irin yadda su ka daɗe su na kai ruwa rana ita da mijin ta.”

 

Majiya ta ce: “An daɗe ana zaman doya da manja a tsakanin ta da mijin. Ba a yi ma zaton auren zai kawo lokacin da su ka rabu ɗin ba saboda tun farkon auren matsalar ta fara kuma ta rinƙa ci gaba, wanda hakan ya haifar da wasu matsaloliin daga baya wanda su kaɗai su ka sani, sai dai kuma Allah.”

 

Majiyar ta ƙara da cewa: “Babbar matsalar da na sani a game mutuwar auren A’isha Tsamiya da mijin ta ita ce, ta na zargin sa da yin soyayya da wasu matan da ita kuma ta ke ganin hakan ba zai yiwu ba. Hakan ya haifar da rigingimu a tsakanin su lokaci zuwa lokaci har daga ƙarshe dai da matsalolin su ka taru su ka yi waya, abin ya kai ga rabuwa.”

 

A bara, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa an ɗaura auren A’isha Muhammad Ali (Tsamiya) da wani mutum mai suna Alhaji Buba Abubakar a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da ke Kano, akasin inda katin gayyatar ɗaurin auren ya nuna, wato masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yan’awaki, a ‘Yankaba, Kano.

 

Ba a yi wani biki ba, sannan sanin ko waye ta aura ya kasance babban sirri wanda ta yi ta nuƙu-nuƙun ɓoyewa har zuwa yau ɗin nan.

 

A yanzu da auren ya mutu, ba a sani ba ko A’isha Tsamiya za ta koma harkar fim ne ko a’a. Amma dai ta ci gaba da kasuwancin da ta saba yi a baya na tallar zannuwa da sauran kayayyakin ƙawa na mata.

 

Ta taɓa mallakar shago a Khairat Plaza da ke daura da sakatariyar NYSC da ke unguwar Janbulo a Kano

Aisha Tsamiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!