Labaran Kannywood

Auren Aisha Tsamiya bai mutu ba, inji ‘yan Kannywood

LABARIN da mujallar Fim ta buga jiya cewar auren tsohuwar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya ya mutu ba gaskiya ba ne, inji ‘yan masana’antar finafinan irin su Ali Nuhu da Abdul Amart Mohammed.

Aisha Tsamiya

Haƙiƙicewar da su ka yi tare da zurfafa bincike da mujallar ta yi ya sa mujallar ta goge labarin daga gidan yanar ta da kuma soshiyal midiya.

Jim kaɗan bayan ɓullar labarin, makusantan tsohuwar jarumar, wadda ta yi aure a Fabrairu 2023, su ka kira wakilan mu a lokuta daban-daban, su na cewa wannan labarin fa kuskure ne domin kuwa A’isha na zaune daram daƙam a gidan mijin ta.

 

Waɗanda su ka kira mujallar sun haɗa da Ali Nuhu, Abdul Amart, da Samira Saj

 

Dukkan su sun nuna cewa su na da kusanci tare da kyakkyawar alaƙa da Aisha da mijin ta mai suna Alhaji Buba Abubakar, kuma ba su daɗe da yin waya da su ba.

 

Samira, wadda ke da kamfanin sayar da tufafi na Samsaj Parlour da ke Abuja, ta ce ita a nata ɓangaren A’isha Tsamiya ɗin ce ma ta tura mata da labarin da aka buga tare da bayyana damuwa. Ita kuma ta yi mata alƙawarin za ta tuntuɓi masu mujallar.

 

Wasu daga cikin ‘yan fim ma da su ka kira labarin da “ƙarya” kai-tsaye sun haɗa da Halima Atete, Saratu Abubakar, Masa’uda ‘Yar’agadas da Sulaiman Costume.

 

Mujallar Fim ta bi dukkan ƙa’idojin aikin jarida wajen tattara bayanai kafin ta rubuta labarin, inda ta samu tabbacin sakin auren daga wasu mutum huɗu, ciki har da ‘yan Kannywood masu sahihin kusanci da A’isha.

 

Haka kuma wani wakilin mu ya yi ƙoƙarin tuntuɓar ta ta hanyar kiran waya da tura mata saƙon tes, amma babu amsa domin, kamar yadda mu ka ji a jiya, ashe ta tafi Umrah ita da wani ƙanen ta.

 

Mujallar Fim ta na bada haƙuri ga ma’auratan saboda rashin jin daɗin da labarin ya jawo masu, tare da tabbacin hakan ba zai ƙara faruwa ba.

 

Mu na yi masu addu’ar Allah ya sa mutu-ka-raba.

Asalin rubutu: Mujallar Fimmagazine

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!