Labarai

An sace wata yarinya mai suna Hanifa Abubakar ƴar shekaru 5 a unguwar Kawaji dake Jihar Kano.

 Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace yarinya wadda bata wuce Shekaru biyar ba a unguwar Kawaji dake Jihar Kano.

An bayyana cewa kuma masu garkuwa da mutanen da suka zo bisa kan babur ɗin adaidaita sahu sune sukayi awon gaba da yarinyar.

Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta tabbatar, yarinyar an ɗauke ta ne da misalin karfe 5pm na yammacin Jiya Asabar a yayinda suka bisa hanyar dawowa gida daga makarantar Islamiyya.

Babu tazara daga gidan iyayen yarinyar zuwa Islamiyyar.

Jaridar Labarai tayi nazarin cewa a kwanakin nan ana samun ƙaruwar sace sacen yara a sassa daban-daban na Nigeria. Lamarin kuma yana ƙara ta’azzara.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!