Labarai/Addini
An Kuma Hana Bada Belin Abduljabbar Kabara – Labarai.com.ng
Wata Babbar kotun Shari’ar Musulunci ta Kofar Kudu a birnin Kano da ke arewacin Najeriya ta sake hana bayar da belin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Lawyan Abduljabbar Nasiru kabara, Muhammad A Mika’il ne ya gabatar da bukatar gaban mai Shar’ia Ibrahim Sarki Yola gabanin kammala zaman kotun a yau.
Gwamnantin jihar Kano ce dai ta ke karar Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin batanci ga Manzon Allah da kalaman da ke tunzura jama’a.
Ibrahim Miniyawa ya tuntubi wakilinmu na Kano, Khalifa Shehu Dokaji, domin jin karin bayani kan zaman kotun.
Www.labarai.com.ng