Al'ajabi

An kama matashi mai sana’ar wankin mota bayan yayi yunƙurin tserewa da motar wani mutum a Jihar Kano.

 An tabbatar da kama wani matashi ɗan shekaru 30 mai sana’ar wankin motoci da yunƙurin tserewa da motar wani kwastomansa.

Mai magana da yawun rundunar ƴan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shine ya bayyana hakan cikin wani bayani na musamman da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa an kama matashin ne a garin Daura, Jihar Katsina ɗauke da motar da ya tsere da ita.

Tun a ranar 30 ga watan Nuwamba ne mutumin da aka sacewa motar ɗan asalin unguwar Badawa ya shigar da rahoto ga hukumar ƴan Sanda dangane da al’amarin.

Har’ilayau, Mista Kiyawa ya bayyana cewa matashin ya amsa lefin da ake zarginsa da shi.

Www.labarai.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!