A DUNIYA

An kama ƙananan yara da laifin yanke Kayin budurwarsu domin yin kuɗin tsafi a Jihar Ogun.

An kama waɗansu yara a Jihar Ogun da laifin kashe budurwar abokinsu tare da yanke kayinta domin yin kuɗin tsafi.

Ƙananan yaran da ake zargi masu suna; Wariz Oladeinde mai shekaru 17, Abdulgafar Lukman mai shekaru 19 da kuma Mustakeem Bolagun 20 sun aikata wannan mummunar aiki ne a ƙauyensu, mai suna Aregba community.

Jaridar DailyPost ta ruwaito cewa a safiyar yau Asabari ne aka kama ƙananan yaran, suna babbaka kayin yarinyar da suka yanke.

Shugaban sintirin ƙauyen mai suna Mista Segun Adewusi shine ya cafke waɗannan ƙananan yara, wanda daga nan ne kuma miƙa su ga jami’an ƴan sanda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!