Uncategorized

Aisha Buhari ta goyi bayan a kashe Abdulmalik wanda ya hallaka Hanifa a bainar Jama’a.

Uwargidan Shugaban Nigeria, Aisha Buhari ta goyi bayan kiraye-kirayen da ake na cewa ya kamata a yankewa Abdulmalik Tanko, malamin da ya kashe yarinya Hanifa hukuncin kisa a bainar Jama’a.

Abdulmalik dai shine, shugaban makarantar Noble Kids, wadda Hanifa take zuwa domin ɗauko karatu.

Ya kuma amsa laifinsa tare da bayyanawa ƙarara cewa shine ya kashe ta, ta hanyar bata guba.

Al’umma suna cigaba da bayyana ra’ayoyinsu cewa, ya kamata Abdulmalik a kashe shi, a bainar Jama’a.

Ita ma Aisha Buhari a nata ɓangaren ta goyi bayan hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
Sabon tallafin ₦50,000
error: Content is protected !!