Labaran Duniya

Ahmed Musa ya bayarda kyautar miliyan 2 ga tsohon Ɗan wasan Nigeria wanda ya koma hayar mota.

Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Nigeria, Kingsley Obiekwu kyautar naira miliyan biyu.

Kingsley yana daga cikin ƴan wasan da suka yi nasarar lashe gasar Olympics wanda aka buga a alif 1996.

Abin mamakin sai gashi tsohon ɗan wasan ya afka cikin halin ƙaƙanakayi saboda rashin wadata, wadda ta kai ya fara hayar mota.

A nasa ɓangaren, Ahmed Musa bai bayyanawa Duniya dangane da kyautar da ya yima tsohon Ɗan wasan ba, amma makusantan shi ne suka bayyanawa manema Labaru kamar dai yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Musa ya aika da kuɗaɗen ne kai tsaye zuwa ga tsohon Ɗan wasan na Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Danna nan ga bidiyon
error: Content is protected !!